Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC) da ta saki fitacciyar ‘yar kasuwar nan Aisha Achimugu, cikin sa’o’i 24.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani dan takaitaccen hukunci da ya yanke a ranar Laraba, ya kuma umurci wadanda ke cikin karar musamman hukumar EFCC da su kai kara kotu a ranar 2 ga watan Mayu domin bayar da karin haske kan bin umarnin kotu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito a baya cewa jami’an hukumar EFCC sun isa kotun tare da Achimugu a ranar Laraba kamar yadda kotu ta bayar da umarni.
Achimugu, wanda jami’an hukumar EFCC mata biyu suka yi mata rakiya, ta isa kotun da misalin karfe 11:35 na safe.
Karin karatu: Tinubu zai kai ziyarar aiki Katsina ranar Juma’a – jami’i
Idan za a iya tunawa,ai shari’a Ekwo, ya umurci yar kasuwar wadda ake zargin ta fice daga kasar, da ta mutunta gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi mata ranar Talata da karfe 12 na rana.
Alkalin wanda ya bayar da umarnin a wani dan takaitaccen hukunci, ya kuma umarci hukumar EFCC da ta saki Achimugu daga ofishinta da ta dawo da ita kotu.
Sai dai an ce jami’an EFCC sun kama Achimugu a lokacin da ta dawo daga kasar waje da misalin karfe 5 na safe kuma aka tsare ta a gidan yari. (NAN)













































