Sayen man fetur a Najeriya ya ragu matuka kasa da shekara guda bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023.
Bayanan da Gidan Talabijin na Channels ya samu daga Hukumar Kula da Hada-hadar Man Fetur ta Ƙasa, NMDPRA, a rahoton ta na dakon mai na Satumba 2024, ya nuna cewa yawan amfani da man fetur a rana a watan Agusta, 2024, ya kai lita miliyan 4.5.
Wannan ya faru ne bayan da yawan man da ake amfani da shi a rana ya ke a matsayin lita miliyan dubu sittin a rana a watan Mayun 2023, a cewar NMDPRA.
Binciken rahoton ya nuna cewa a cikin jihohi 36 na tarayyar Najeriya, jihohi 16 ne kawai suka samu rabon kason mai daga kamfanin man fetur na kasa, NNPCL.
Wannan yana nufin cewa su kuma jihohin da ba su samu man ba sun fuskanci ƙarancin sa a cikin watan Agusta.