Gwamnatin Jihar Kano ta yi karin girma ga ma’aikata sama da 230

Hukumar kula da ma’aikata ta Jihar Kano ta amince da Karin girma ga manyan jami’an gwamnati 231 daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati dake fadin Jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban hukmar Dakta Umar Shehu Minjibir ne ya bayyana hakan bayan da hukumar ta yi zaman ta na farko a ranar 5 ga watan Oktoban daya gabata, tun bayan zaman sa shugaban hukumar.

A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Musa Garba ya fitar a ranar Juma’a, ya ce shugaban ya bayyana cewa sauran batutuwan da aka cimma sun hada da na canjin wurin aiki wanda tuni aka amince da na mutum 50 sai batun sauyin suna guda 1, da sauran su.

Ta cikin sanarwar Dakta Umar Shehu Minjibir ya kuma umarci ma’aikatan da abin ya shafa musamman wadanda aka kara musu girma da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu domin ganin an samar nagarta a aikin gwamnatin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here