Takarar Kano ta Arewa: Gwarzo da Ganduje sun gana da Shettima a yayin da ake ci gaba da yarjejeniya a APC

IMG 20260512 WA0012 750x430

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a Abuja, kwanaki kadan bayan an tantance shi a matsayin dan takarar kujerar Sanata ta Kano ta Arewa a karkashin APC.

SolaceBase ta ruwaito cewa wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin cimma yarjejeniya a cikin APC a Kano, wadda fadar Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ke karfafawa, domin rage fafatawa a cikin gida gabanin zaben 2027.

Wani dan takarar kujerar Kano ta Arewa, Dr. Mahmoud Baba Bichi, wanda a baya ya nuna niyyar tsayawa takara a zaben Sanatan Kano ta Arewa, daga baya ya janye bayan shiga tsakani da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Gwarzo ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa Facebook a ranar Talata, inda ya ce ganawar ta gudana ne a gidan Mataimakin Shugaban Kasa da ke Abuja.

A cewarsa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi, Abba Abubakar Kabir Bichi, sun halarci ganawar.

“A yau, tare da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi, Abba Abubakar Kabir Bichi, mun gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Mai Girma Kashim Shettima,’’ sakon ya ce.

“Mun tattauna kan siyasa da harkokin siyasa a Kano ta Arewa, kuma ya yi mana fatan nasara da ci gaba a tafiyarmu ta siyasa,” in ji Gwarzo.

A yanzu haka Sanata Barau Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ne ke rike da kujerar Sanatan Kano ta Arewa, kuma yana neman sake tsayawa takara a zaben 2027.

Shigowar Gwarzo cikin masu memam na nuni da yuwar samun fafatawa tsakanin manyan mutane a jam’iyyar, duk da kokarin shugabannin jam’iyyar na cimma yarjejeniya domin kiyaye hadin kai a cikin APC a jihar.

Masu sharhi kan siyasa na cewa sakamakon tattaunawar yarjejeniya zai iya tantance ko jam’iyyar za ta shiga zaben fidda gwani ko kuma ta fitar da dan takarar masalaha a zaben da ke tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here