Ribadu na nan a matsayinsa na NSA– Majiya daga Fadar Shugaban Kasa

IMG 20260512 135333

Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaron (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, bai yi murabus daga mukaminsa ba biyo bayan kirkirar Ofishin Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa kan Tsaron Kasa, in ji wata babbar majiya kan harkokin tsaro da ke da alaka da Fadar Shugaban Kasa.

Majiyar, wadda ta yi magana da PRNigeria ba tare da an bayyana sunanta ba, ta bayyana rahotannin da ake hadawa na zargin murabus din Ribadu a matsayin karya, mara tushe, da rudani.

A cewar majiyar, nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa mai ritaya a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Tsaron Kasa na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa tsarin tsaron Najeriya da inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Famadewa ya kasance tsohon Jami’in Ma’aikata na Musamman (PSO) ga Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa lolacin Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, tsakanin 2015 zuwa 2021.

Majiyar ta bayyana cewa sabon ofishin da aka kirkira an tsara shi ne domin cike gibin tsarin tsaron da ake da shi, kama da hukumar Lura da Shige da Fice, hukumar dake Tsaro da Kare Kadarori da ta Tsaron Sufuri da Ayyukan Leken Asirin Cikin Gida wadanda ba sa karo da nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaron (ONSA).

“Jita-jitar da ke cewa Mallam Nuhu Ribadu ya yi murabus karya ce gaba daya kuma a ki amincewa da ita,” in ji majiyar.

Jami’in ya kara da cewa barazanar tsaro da ke kara kunno kai, ciki har da ta’addanci, fashi da makami, laifukan yanar gizo, laifukan ketare iyaka, da ta’asar tattalin arziki, na bukatar tsari mai hadin kai daidaito a cikin tsarin tsaron kasar.

Majiyar ta kara bayyana cewa Ribadu na ci gaba da samun amincewar Shugaba Tinubu kuma yana ci gaba da shiga cikin daidaita ayyukan tsaron kasa, gudanar da leken asiri, da hadin gwiwa tsakanin hukumomi a fadin kasar.

Majiyar ta Fadar Shugaban Kasa ta roki ‘yan Najeriya da su yi watsida labaran hasashe da za su iya haifar da tashin hankali ko rudini da ba a bukata a harkokin tsaron kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here