Sabon rikici ya barke tsakanin Hukumar ‘Yan Sanda, Babban Sifeton Yan sanda

IGP alkali
IGP alkali

Babban Sifeton ‘yan sandan Kasar nan, Alkali Baba Usman, da hukumar ‘yan sanda sun sake samun sabani game da daukar aikin ‘yan sanda.

Hukumar ‘Yan sandan ta bude shafinta don daukar aikin ‘yan sanda na shekara ta 2022 tare da sanya tallan daukar aikin a jaridun kasar nan.

Sai dai a martanin da rundunar ‘yan sandan Kasar ta yi kan lamarin, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan talla.

A wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce tallan bai da alaka da rundunar ‘yan sandan Najeriya, kuma bai dace da tsarin daukar aikin ‘yan sanda ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Rundunar ‘yan sandan na son sanar da jama’a masu kishin kasa cewa ba ta fara daukar aikin ‘yan sanda a shekarar 2022 ba, sabanin yadda hukumar ‘Yan sandan tasa aka buga a shafi na 21 na Jaridar Daily Sun ta ranar Alhamis 11 ga watan Agustan Shekarar 2022 ba.

“Hakazalika rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa babu shakka tallan ba shi da alaka da rundunar ‘yan sandan Najeriya, gaba daya.

Shafin internet da aka fitar domin masu sha’awa wato http://www.recruitment.psc.gov.ng – ba shi da alaka da Rundunar ‘Yan sandan Najeriya.

“Rundunar ‘yan sandan ta na kira ga duk masu ruwa da tsaki da masu niyyar neman aikin Kan su yi watsi da bayanan da ke cikin jaridar da kuma shafukan internet din da aka bayar saboda ba na rundunar bane.

“Rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a sanar da fara aikin daukar ma’aikatan na shekarar 2022 ta shafin daukar aiki na rundunar wato– https://policerecruitment.gov.ng, da Kuma shafin internet na rundunar ‘yan sandan Najeriya wato- https: //www.npf.gov.ng da Kuma bayar da sanarwar daukar aikin a jaridu na kasa da sauran kafofin yada labarun ‘yan sanda a lokacin da ya dace.”

Idan dai za a iya tunawa, tsohon Sifeton Yan Sandan Kasar nan Mohammed Adamu da Shugaban hukumar’Yan sandan, Alhaji Musiliu Smith sun yi takun-saka kan wadanda doka ta bawa damar gudanar da aikin daukar ma’aikata.

Hukumar dai ta maka tsohon Sifeton Yan Sandan da rundunar ne a gaban kotu saboda gudanar da aikin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda dubu 10,000 a shekarar 2019.

3 SHARHI

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here