Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya ce ba butulci kawai aka yi masa ba, amma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya wulakanta shi.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a ofishin gidauniyar Kano, dake kan titin Jami’ar Bayero a Kano, Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya ce tasa ta kare a Jam’iyyar NNPP.
A cewarsa ya yi nadama yayin da aka bashi tikitin takara a jam’iyyar bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC, babu wani magoyin bayansa kuma da jam’iyyar ta ba shi tikitin takara.
Da yake tunawa da dangantakarsa da Kwankwaso a jam’iyyar NNPP, Shekarau ya ce a ranar 5 ga Mayun Shekarar nan ta 2022 tun kafin su koma jam’iyyar NNPP, “Ni da kaina na hadu da shi a gidan sa, kuma mun tattauna sosai kan niyyata ta bin shi zuwa sabuwar jam’iyyarsa kuma ya nuna farin ciki matuka.
“Kazalika a ranar 11 ga Mayun Shekarar nan ta 2022, na sake haduwa da shi- domin tun haduwarmu ta karshe, ba mu sake haduwa ba, kuma na tuna masa wata shawara da na mika masa a ganawarmu ta karshe.
“Shawarorin sun kunshi jerin sunayen magoya bayana da ke neman mukamai daban-daban, kuma da na tunatar da shi game da hakan, sai ya ce yana sane da hakan kuma tabbas za a yi wani abu.
“Hakazalika, a ranar 16 ga watan Mayun Shekarar nan ta 2022, Kwankwaso ya zo gidana da misalin karfe 9:00 na dare inda muka tattauna batutuwa irin na baya, har ma ya kira mutane hudu da suka hada da Abba Kabir Yusuf da aka nada shugaba da Kawu Sumaila da Alhassan Rurum ya gabatar min da su a matsayin wadanda za su rubuta sunayen Yan takara.
“A taron da aka yi kafin na sauya sheka, Kwankwaso ya zo da fom dina na Sanata ni kadai, inda ya shaida min cewa ni ne na fara karba, na tambaye shi Ina na wadanda ke goyon bayana ya ce za a yi daga baya.
“Tun daga wancan lokacin Kwankwaso ya ci gaba da yaudarata, daga baya ya ce mun makara magoya bayana su shiga jerin sunayen, kuma babu abin da zai iya yi,” in ji Shekarau.
‘’Don haka za ku ga cewa sama da watanni uku, kwamitin da aka kafa bai iya yin komai ba game da shawarwarinmu.’’
“Ba zan taba zama a jam’iyyar rashin adalci ba. Daraja ta ita ce mafi girma ga duk wani matsayi na siyasa da zai sa in yi butulci ga jama’a ta. Babu wanda zai yi amfani da matsayi ko kudi a kan mutuncina.
“Ni mutum ne mai mutunci da rikon amana amma dan takararsa na gwamna (Abba Yusuf) wanda aka dora wa alhakin duba wuraren da zai dauki mutanena mukamai daban-daban bai taba yin haka ko ma kiran taro a yini daya ba balle ya yarda dani da magoya bayana su yi takara ba.
“Ba wanda zai yi amfani da kudi don canza akala ta. Na yi gwamna shekara takwas a Kano kuma mutane sun yi imani da gaskiya ta.
“Har yanzu ina zaune a gidan haya a Abuja ban taba ware wa kaina fili ba a lokacin da na yi Gwamna a Kano kuma ina kalubalantar duk wanda ya san filina Kan ya tona asirinsa.”
Tsohon gwamnan ya koka da cewa duba da irin wadannan yaudara da ma wasu da dama ba shi da gurbi a jam’iyyar NNPP, inda ya ce ra’ayinsa na siyasa shi ne ya rika tafiya da magoya bayansa, inda ya ce duk wani yunkuri na jefar da su ba zai yarda da shi ba.
Ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu hakuri yayin da ake dakon rahoton da Majalisar Shura, za ta gabatar, bayan yin nazari nan ba da jimawa ba tare da daukar mataki na karshe.
Shekarau ya tabbatar da cewa tuni wasu jam’iyyun siyasa da dama ke tattaunawa da shi da mambobinsa.













































