Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan karar dake neman hana Stella Odua, yin takara

Stella oduah final 0
Stella oduah final 0

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta sa ranar 30 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci kan karar da aka kai sanata Stella Oduah, domin neman kotun ta hanata yin takara a zabe shekarar 2023.

Oduah tana neman kujerar sanata a shiyar Anambra masu gabas a kakar zaben bana, kujerar da ta ke kai tun daga shekarar 2015 har zuwa yanzu.

Mai shara’a Inyang Ekwo tasa ranar ne bayan wanda yake kara da wacce ake kara sun gabatar da hujjojin su.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaitu cewa John Emeka, wanda ya shiga zaben fitar da gwani da hukumar zabe ta kasa ta kula dashi a ranar 27 ga watan Mayu, ya yi karar sanata Oduah, jam’iyyar PDP da kuma INEC.

Emeka ya zargi Oduah da yin karya yayin cike fom din na gani ina so na APC da kuma fom din yin takara na INEC.

A cikin karar mai lamba ta FHC/ABJ/CS/841/2022, Emeka ya ruki kotu data dakatar da Oduah daga yin takara bisa zargin ta da karya yin bautawa kasa NYSC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here