Gwamnatin jihar Katsina ta ce wanda ya lashe gasar karatun Alkur’ani, Abdussalam Rabi’u-Faskari ds mahaifinsa da dan’uwansa suna nan a raye amma suna hannun wadanda suka sace su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu, Dr Bala Salisu-Zango ya fitar ranar Juma’a a Katsina.
Idan dai za a iya tunawa dai an yi garkuwa da mutanen kwanaki biyu da suka gabata a hanyarsu ta zuwa Faskari daga Katsina bayan da Gwamna Dikko Radda ya karrama su saboda bajintar da ya nuna a gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a Kebbi.
A cewar Salisu-Zango matashin zai wakilci Najeriya wajen karatun kur’ani baki daya a gasar da za a yi a duniya.
Karanta: Katsina: Gwamna Radda Ya Bawa Mai Digirin Da Yake Siyar Da Ruwa A Kan Titi Aiki
Salisu-Zango ya ci gaba da cewa, ya zuwa ranar Juma’a, masu garkuwa da mutanen suna neman a biya su kudin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansu.
Kwamishinan ya ruwaito Radda yana bayyana sace matashin hazikin dalibin, tare da mahaifinsa da dan uwansa a matsayin abin takaici.
Daga nan sai Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro da su sanya hannu a kai don ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa.
Radda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
Daga karshe ya yi kira ga jama’a da su kara yi wa Rabi’u-Faskari addu’a Allah ya ba su lafiya da kuma sauran wadanda ke hannun miyagun masu garkuwa da mutane.(NAN)













































