Gwamna Zulum ya raba motoci da gidaje ga hukumomin tsaro

IMG 9233 750x430

A ranar Juma’ar da ta gabata ne babban sifeton ‘yan sandan kasar nan Kayode Egbetokun, ya kaddamar da rabon motocin aiki guda 110, babura 500, da gidaje 280 ga hukumomin tsaro a Borno.

Shirin wanda gwamna Babagana Umara Zulum ya jagoranta na da nufin inganta ayyukan tsaro da kyautata jin dadin jami’an tsaro a fadin jihar.

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Maiduguri, IGP ya yaba wa gwamnan bisa ci gaba da goyon bayansu, inda ya bayyana shi a matsayin gwamna mai taka rawar gani wajen magance matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas.

IGP din ya bada tabbacin cewa za’a raba sabbin kadarorin da aka bayar nan take domin karfafa ayyukan tsaro a fadin jihar Borno.

Karin karatu: An sauya sunan jami’ar jihar Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim

A nasa jawabin, Zulum ya ce shirin na daga cikin kudirin gwamnatinsa na karfafa ayyukan tsaro a jihar.

A cewar sa, tsaro ya kasance ginshikin farfadowa da ci gaban Borno, inda ya yi alkawarin ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro.

Zulum ya kuma amince da jagorancin shugaba Bola Tinubu wajen tallafawa ayyukan tsaro a fadin kasar nan, musamman a Borno.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta karbi motoci 60 daga cikin 110, yayin da sojojin Najeriya za a ware musu motoci 50 da babura 500.

Bugu da kari, ‘yan sandan za su karbi gidaje 220 a rukunin Mai Mala Buni, 20 a Kashim Shettima da kuma wasu 40 a Wulari, duk a Maiduguri.

Manyan jami’an tsaro sun halarci bikin, ciki har da kwamandan Operation Hadin Kai, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, da kuma manyan jami’an ‘yan sanda, sojoji, da na ‘yan sanda. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here