Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce kawo yanzu ta yi wa sabbin mambobinta kusan 53,000 rajista a Adamawa.
Mista Phineas Elisha, Shugaban riko na jam’iyyar na jihar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai ranar Talata a Yola.
Elisha ya ce jam’iyyar na da dimbin mabiya a jihar da kuma musamman a matakin kasa inda ya ce jam’iyyar ta kuma samu karbuwa a sassa daban-daban na jihar.
“Sauran jam’iyyun siyasa na cikin tashin hankali saboda suna tsoron kada NNPP ta kwace jihar.
“Asalin wannan bayanin kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bukata shi ne sanar da jama’a ayyukan jam’iyyar, mun yi wa sabbin mambobi sama da 53,000 rajista a jihar.
“Yau 15 ga Maris, bisa ga umarnin INEC. Zamu gudanar da taro a fadin kananan hukumomi 226 dake kananan hukumomin jihar 21.
“Daga ranar 19 ga Maris zuwa 21 ga Maris, za mu gudanar da tarukan kananan hukumomi a dukkan kananan hukumomin 21 da kuma taron na jiha kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya da kuma sa ido na INEC,” in ji Elisha.
Ya ce manufar jam’iyyar ita ce tabbatar da zaman lafiya, daidaiton jinsi da ci gaba baya ga tabbatar da samar da abinci a kasar nan.
“A ranar 28 ga Maris, jam’iyyar za ta gudanar da babban taron shiyyoyin da za a kammala babban taron kasa a ranar 30 ga Maris,” in ji shi.
Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta tsayar da ‘yan takara a dukkan mukaman zabe a zaben 2023 mai zuwa.
Kungiyar siyasa ta National Movement karkashin Sanata Rabi’u Kwankwanso, tsohon gwamnan jihar Kano, a kwanan baya ta ayyana jam’iyyar NNPP a matsayin jam’iyyar da zasu yi shiga a lokacin babban zabe na 2023.