Dokar Zaɓe ta keɓance INEC daga hukunta ƴan siyasa kan fara Kamfen da wuri – Mahmood Yakubu

Mahmood Yakubu new 750x430

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce tana da ƙarancin iko na doka wajen hukunta ’yan siyasa da suka fara yaɗa kamfen kafin lokacin da doka ta tanada.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan matsalar kamfen da wuri.

Ya ce sashe na 94(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana kamfen kafin kwanaki 150 da zaɓe, amma bai tanadi hukunci ga masu karya wannan doka ba.

Yakubu ya ce abin da doka ta fayyace shi ne tara har zuwa Naira 500,000 ga wanda ya yi kamfen cikin sa’o’i 24 na ranar zaɓe, amma babu hukunci ga waɗanda suka yaɗa kamfen kafin lokacin da ya kamata.

A cewarsa, hakan ya sa ’yan siyasa ke ci gaba da shirya gangami, sanya tallace-tallace a tituna da kafafen yada labarai, duk da rashin bin ka’idar doka.

Ya ce irin wannan yaɗa kamfen da wuri yana hana INEC damar bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗen kamfen, tare da kawo cikas ga tsarin da ya kamata.

Saboda haka, hukumar ta gayyaci ’yan majalisar dokoki, shugabannin jam’iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula domin tattaunawa kan mafita, musamman yanzu da ake sake duba dokokin zaɓe a majalisa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here