Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da killace gidan wani dakataccen shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, a cikin daren Lahadi.
Idan dai za a iya tunawa, ‘yan sandan sun ajiye motocinsu ne a kusa da gidan Muhuyi Magaji Rimingado, dake kan titin Yahaya Gusau, inda suka yi masa kwanton bauna da misalin karfe 7 na dare a ranar Lahadi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Solacebase a ranar Litinin, jami’in yada labarai na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ‘’Mutanenmu sun je gidan ne domin yi masa gayyata amma ba mu samu damar yin hakan ba.
Ya ce gayyatar ta biyo bayan umarnin kotu ne na yin watsi da karar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya shigar yana neman a dakatar da kama shi.
‘’Saboda haka mutanenmu suka yanke shawarar zama a gidan domin su yi masa gayyatar da muka samu cewa yana gidan,’’ in ji Kiyawa.
Da aka tambaye shi game da harbin da ake zargin ‘yan sanda sun yi, Abdullahi Kiyawa ya shaida wa Solacebase cewa ‘yan sandan ba su yi harbi ba, inda ya nanata cewa babu bukatar hakan.
An dakatar da Mista Rimingado ne a watan Yulin shekarar da ta gabata bisa zargin badakalar kudi da karin kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da dangin gwamnan Kano Ganduje.
Solacebase ya yi kokarin tuntubar Muhuyi Rimingado don jin ta bakinsa game da labarin amma layukan wayarsa a kashe suke.













































