A yau Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallami tsohon ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati Kabiru Turaki, tare da wanke shi daga zargin karkatar da kudade.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a cikin hukuncin da aka yanke kan karar, ya ce hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kasa alakanta Turaki da wadanda ake tuhuma da laifukan da ke kunshe cikin tuhume-tuhume 16, inda ya ce masu gabatar da kara sun kasa kafa hujja kan zargin.
Mai shari’a Ekwo ya ce wadanda ake tuhumar sun kori dukkanin shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar a kan lamarin yayin sauraron shari’ar, inda ya bayyana shaidu 12 da EFCC ta dogara da su a matsayin shedun gaibu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa hukumar EFCC na tuhumar tsohon ministan da wasu mutane da laifin almundahana naira miliyan 715 ba bisa ka’ida ba.













































