Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta bayyana mamayar da ‘yan ta’adda suka yi a filin jirgin Kaduna, ranar Asabar, a matsayin manuniyar yadda matsalar tsaro ta tabarbare a Najeriya.
Afenifere, a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Jare Ajayi, ya fitar, ta koka da cewa abin da ya faru a Kaduna a ranar da jam’iyyar APC ke gudanar taronta a Abuja, ya nuna yadda wasu ke son mayar da Najeriya kamar kasar Afganistan duba da yadda ‘yan ta’adda ke fadada ayyukan su zuwa muhimman wurare a cikin Najeriya.
Idan za a iya tunawa, ‘yan ta’addan da ake zargin sun haura 200, sun mamaye filin jirgin saman Kaduna a ranar Asabar, 26 ga Maris, 2022, inda suka kashe ma’aikatan jirgin tare da raunata da dama.
Hakan kuma ya tilasta jinkirin tashin jirage ciki har da wanda zai je Legas.
Mai magana da yawun kungiyar ta Afenifere ya ce: “Abin takaici ne cewa wadannan ta’addancin tsaro sun faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke tabbatar mana da cewa ta kawo kashen wannan matsalar.
A cewar Kungiyar Yakamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta baiwa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sanda, su baiwa jami’an tsaron da ake da su karfi, su daina yiwa ‘yan ta’adda dauki da safarar yara, sannan dole ne a gaggauta aiwatar da wadannan don kada Najeriya ta zama kamat Afghanistan.”












































