Kano: Karnuka sun cinye sassan jikin jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a unguwar Gaida

Jaririya, Gaida, Kano, Kumbotso, sabuwar, haihuwa
A ranar Alhamis da karfe 6:50 na safe ne aka wayi gari da ganin gawar wata Jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a Unguwar (Gaida Maharba) Layin Sabis da ke...

A ranar Alhamis da karfe 6:50 na safe ne aka wayi gari da ganin gawar wata Jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a Unguwar (Gaida Maharba) Layin Sabis da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da al’umma suka fara futowa daga gidajensu, inda suka iske gawar jaririyar a bakin hanya.

Karin labari: Kungiyar kwadago ta NLC a Kano ta koka da koma bayan fansho da ba a biya

Saidai wasu shaidun gani da ido sun bayyana lamarin a matsayin rashin imani da tausayi wanda ake kyautata zaton cikin dare aka bi aka jefar da jaririyar.

Jaridar SolaceBase ta tuntubi mai unguwar yankin, Malam Saleh Sa’idu, kan sahihancin lamarin, mai unguwar ya tabbatar da cewar tabbas lamarin ya faru kuma shi ma ya kadu da ganin gawar sabuwar jaririyar.

Karin labari: Gwamnatin Zamfara ta ja hankalin ma’aikatan da ke karbar albashi da yawa

“Tabbas wannan lamari ya faru kuma ni kaina nayi matukar kaduwa da tashin hankali dana iske wannan lamari da idanu na.

“Bayan faruwar lamarin, na yi kokarin sanarwa da Dagachi da Hakimi, sannan na yiwa jami’an tsaron ‘yan sanda na Panshekara karin haske dangane da lamarin, wanda daga nan ne suka ba da damar yiwa gawar sutura”.

Karin labari: NDIC: Hukumar Inshora ta sanar da sake duba matsakaicin inshorar kuɗi na bankuna

Sa’idu, ya kara da cewa, “Wannan karo na uku kenan ana ganin makamancin irin wannan rashin imanin a yanki na, amma dai na yanzun yafi kowanne muni sosai fiye dana baya.”

Sai dai a karshe, Saleh, ya bayyana ba’a tabbatar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba, amma dai sun barwa jami’an tsaro da kwamitin unguwa komai a hannunsu domin ci gaba da yin buncike.

Karin labari: Kotu ta ba da umarnin sauya sabis na odar wucin gadi kan Multi-Choice

“Har yanzu ba’a tabbatar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba, amma mun barwa jami’an tsaro da kwamitin unguwa komai a hannunsu domin ci gaba da yin buncike kan wannan mummunar lamarin” in ji Mai Unguwar.

Ba wannan ne karo na farko da ake ganin jarirai musamman sabbin haihuwa a wasu yankuna na birnin Kano da wajen birnin ana jefar da su ba, ana tsintar wasu da ransu wasu kuma a tsinci gawarsu ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here