Da ɗumi-ɗumi: Murtala Garo ya yi murabus daga mukaminsa domin yin takarar gwamna

Murtala Garo
Murtala Garo

Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Kano Murtala Sule Garo, ya yi murabus daga mukaminsa.

Solacebase ta ruwaito cewa murabus ɗin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da wa’adin ajiye muƙami don tsaya wa takara a zaɓen baɗi inda ya buƙaci masu ra’ayin da su yi murabus daga ranar 18 ga Afrilu ko kuma kafin ranar.

Kwamishinan dai na ɗaya daga cikin masu neman kujerar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Garo, ya bayyana a cikin wasiƙar murabus ɗin cewa ya kasance abin alfahari da aiki ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Ganduje tun shekarar 2014.

“Na rubuta cikin ƙasƙantar da kai da godiya ina mai miƙa takardata ta murabus a matsayin Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu na Kano.”

“Mai girma gwamna, ya kasance abin farin ciki matuƙa gaya wajen yin aiki kai tsaye a kuarƙashin jagorancinka da kulawa tun daga shekarar 2014 lokacin da aka zaɓe ni a matsayin shugaban ƙaramar hukuma da kuma shawarar da ka yanke na nada ni a matsayin kwamishina a gwamnatin ka, Waɗannan shekaru sun ba ni dama mai wuyar samun damar yin amfani da basirar gudanarwa da basirar siyasa.”

“Ko shakka babu wannan gwamnati mai ci a ƙarƙashin inuwar ku ta yi tasiri ga rayuwar al’ummar jihar Kano kuma ina alfahari da kasancewa cikin gagarumin ci gaban da wannan gwamnati ta samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata, Yayin da nake gode wa mai girma gwamna don ba ni wannan babban aiki.”

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here