Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya nesanta kansa da fom din takarar shugabancin Kasa a jam’iyyar APC da wata kungiya ta saya ta bashi.
Cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran tsohohon shugaban kasar ya fitar sa’o’i kadan bayan da kungiyar ta sayi fom din a kan Naira miliyan 100, Jonathan yaki aminta da matakin, yana mai jaddada cewa shi ba dan jam’iyyar APC ba ne.
“A cewar sanarwar al’umma su yi watsi da abin da kungiyar ta aikata, domin ba da sanin Goodluck Jonathan ta yi ba.”
A ranar Litinin da yamma ne dai wata bakuwar kungiya mai suna ‘Kungiyar Fulani’ ta saya wa tsohon shugaban kasar fom din, duk da cewa bai taba bayyana cewa ya koma jam’iyyar APC ba.
Jim kadan ne kuma ofishinsa na yada labarai ya sanar cewa, “Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya samu labarin wata kungiya mai suna “Fulani Group” ta sayi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da sunansa.
“Muna sanar da jama’a, musamman al’ummar Najeriya cewa Goodluck Jonathan ba shi da masaniya ko wata alaka da sayen fom din da aka yi da sunansa, hasali ma ba shi da kowace irin alaka da kungiyar.
“A sani cewa a halin yanzu Jonathan ba dan jam’iyya APC ba ne, don haka ba zai yiwu ba ya yi na’am da irin wannan tayi daga masu wannan yunkuri.”
Duk da haka sanarwar ta bayyana godiyar Jonathan ga ’yan Najeriya da ke ta kiraye-kirayen ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023 da ke kara karatowa.
Ofishin ya ce, “Muna kara jaddada cewa a halin yanzu ba shi da aniyar karbar wannan tayin da ake yi masa, duk da cewa akwai masu ganin cewa fitowar tasa ita ce kishin Kasa.”
Wasu majiyoyi masu tushe sun shaida wa Manema labarai cewa wasu gwamnoni biyu a jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya ne kan gaba a yunkurin ganin Jonathan ya gaji Buhari a 2023.
Daya daga cikin gwamnonin, wanda a baya-bayan nan suka yi ruwa da tsaki a APC, ya fito ne daga yankin Arewa ta Gabas, dayan kuma daga Arewa ta Yamma.
Majiyar ta ce kowanne daga cikin gwamnonin biyu na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.













































