Kusan jam’iyyun siyasa 18 karkashin inuwar gamayyar Jam’iyyu ta Inter-Party Advisory Council (wato IPAC) sun bukaci hukumar Zaben Najeriya INEC da ta duba yiwuwar kara wa’adin ranar da za a kammala zabukan cikin gida na fidda gwanayen ‘Yan takara, maimakon ranar 3 ga watan Yuni da ta sanya a baya.
Shugaban gamayyar Jam’iyyun na kasa Injiniya Sani Yabagi, shi ne ya yi wannan rokon yayin da hukumar Zaben ke tattaunawa da Jami’yyun Siyasar Kasar ranar Talata a Birnin Tarayya Abuja.
Jam’iyyun sun bukaci hukumar zaben INEC da ta kara kwanaki 37 akan ranar da ta sanya a baya.
Muna tafe da karin bayani…..












































