Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Majalisar dokokin jihar Osun za ta aika da kudiri ga gwamna Ademola Adeleke domin kara albashin wasu masu rike da mukaman siyasa.
Kakakin majalisar, Adewale Egbedun ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Litinin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya bayar da rahoton cewa, an gabatar da kudirin karin albashi mai taken, masu rike da mukaman siyasa na jihar Osun sun sake duba kunshin albashi (gyara mai lamba 2) Bill 2024 a gaban majalisar a ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.
Karin labari: ‘Yan gwadago za su halarci taron tattaunawa a kan mafi karancin albashi
Shugaban masu rinjaye kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Ede ta Arewa, Kofoworola Adewunmi, ya gabatar da kudirin ga majalisar a matsayin wani kudirin doka mai zaman kansa.
Da yake karanta manufofin kudirin dokar, Adewunmi ya bayyana cewa karo na karshe da aka sake duba albashin ma’aikatan gwamnati da siyasa a jihar a shekarar 2007.
Ya ce albashin da aka gindaya wa masu rike da mukaman gwamnati a cikin kundin tsarin albashin ma’aikatan gwamnati na jihar Osun na shekarar 2007, duk da haka, bai dace da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu ba.
Karin labari: Majalisar ministocin Iran ta yi sabon zaman gaggawa bayan mutuwar shugaban kasar
“Za ku yarda da ni cewa gaskiyar tattalin arziki a halin yanzu ba daidai ba ne da abin da aka samu shekaru 17 da suka wuce lokacin da aka zartar da doka.
“Saboda haka, ya zama wajibi a duba sama, albashin wasu masu rike da mukaman gwamnati ko siyasa don inganta rayuwarsu wanda ya yi daidai da ajandar maki biyar na Gwamna Ademola Adeleke.
Karin labari: “Ma’aikata za su zauna a gida maimakon karbar Naira Dubu 48,000” – NLC
“Bugu da kari, kudurin Majalisar Jiha da aka yi a ranar 8 ga Mayu, 2008, inda aka yi nazari mai zurfi kan kunshin biyan albashin wasu ma’aikatan gwamnati wadanda ba su cikin kwamitin tattara kudaden shiga, kamar yadda gwamnatin jihar ta tsara. an kara nazari kuma an ci gaba da aiki a karkashin wannan doka,” inji shi.
Hakazalika ya kuma bayyana cewa karin albashin bai shafi ko kuma ya biya albashin ‘yan majalisar ba, inda ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar na duba albashin ‘yan majalisar dokoki bisa ka’ida.