‘Yan bindiga sun sace mutum 16 yayin da ‘Yan sanda suka ceto mutum 4 a Abuja

'yan bindiga, sace, mutum, 'Yan sanda, Abuja, ceto
Wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadi sun kai hari a unguwar Dawakin Rock Heaven da daura da Gwarimpa Estate a Abuja inda suka sace mazauna yankin 16. SolaceBase...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadi sun kai hari a unguwar Dawakin Rock Heaven da daura da Gwarimpa Estate a Abuja inda suka sace mazauna yankin 16.

SolaceBase ta bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai harin ne da misalin karfe 7.30 na dare a wani samame da ya dauki tsawon mintuna 30 ana yi.

‘Yan ta’addan da aka ce sun kai wa al’ummar garin hari ne a cikin motoci hudu sun kunshi maza da mata wadanda suka rika harbin iska kafin su kai farmaki kusan gidaje shida.

Karin labari: Majalisar Osun ta ba da shawarar karin albashi ga masu rike da mukamin siyasa

Shugaban kungiyar Dawaki Rock Heaven Community, Alhaji Tunde Abdulraheem ya shaida wa SolaceBase ranar Litinin da rana cewa bayan kidayar kawunansu, sun gano cewa an sace mazauna 16.

”An sace mata takwas da maza 4 da yara 4 yayin harin da ya dauki kusan sa’a daya,”Abdulraheem ya shaidawa SolaceBase.

Karin labari: ‘Yan gwadago za su halarci taron tattaunawa a kan mafi karancin albashi

Ya ce 3 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun tsere daga hannun ‘yan bindigar da suka yi mu’amala da su zuwa tsaunuka da ke kewayen al’umma yayin da jami’an tsaro suka ceto wasu 4 bayan artabu da ‘yan ta’addan.

Da take tsokaci game da harin, mai magana da yawun ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Benneth Igweh, ya jagoranci ‘yan sanda zuwa wurin, inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutanen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here