Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Lagos, ta bada umarnin kamo wasu ‘yan kasar waje da suke gudanar da kasuwancin su a Najriya, Nabil Maukarzel da kuma Halawi Fidaa bisa kin bin umarnin kotun na su bayyana a gabanta tun 2021, kan zargin damfara wace ta kai kimanin biliyan N9.4.
Ana zargin Maukarzel, wanda dan Labanan ne da kuma Fidaa dan kasar faransa bisa mallakr kudin damfara wanda suka kai N9,442, 788,578.93, a bankin ECO Bank.
Kuton bada umarnin cewa duk inda aka gansu, a kamasu a kai su ofishin ‘yan sanda mafi kusa.