Gidan gyaran halin Kuje: ‘Yan Sanda sun kama wani mutum dan shekara 60 da ya tsere a kan hanyarsa ta zuwa Kano

Ali Shuaibu 750x430 1
Ali Shuaibu 750x430 1

An kama wani da ake zargi yana cikin wadanda suka tsare daga gidan ajiya da gyaran hali na Kuje, a jihar Kaduna akan hanyarsa ta zuwa jihar Kano.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce wanda ake zargin, Ali Shuaibu mai shekaru 60 dan asalin jihar Kano ne kuma wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wadanda suka gudu daga wurin da ake tsare da su a lokacin da Boko Haram suka kai hari gidan.

“Wanda ake zargin Ali Shuaibu dan shekara 60 kuma dan asalin jihar Kano, jami’an ‘yan sanda ne suka kama shi a wani wuri a Kaduna, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano bisa samun bayanan sirri.

“Wanda ake zargi daga bincike na farko ya nuna cewa yana cikin fursunonin da suka tsere a harin da aka kai a tsakiyar cibiyar tsaro ta Kuje.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Kaduna CP Yekini A. Ayoku psc, mni ya bayar da umarnin a aiwatar da ka’idojin da suka dace kafin mika wanda ake zargin ga hukumar kula da gyaran hali ta Kasa domin a tura shi wurin da ya dace.

“Ya kuma umurci jami’an da kada su yi kasa a gwiwa a kokarinsu na magance duk wani nau’in laifuffuka da ake aikatawa a sassan jihar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here