Nasarar Osun: Ka fara kasha wutar Gidanka tukunna, Matasan PDP na Kano sun mayarwa Gwarzo Martani

Senator Bello Hayatu Gwarzo
Senator Bello Hayatu Gwarzo

Kungiyar matasan jam’iyyar PDP ta Kano wato PDP Youths in Action sun mayar da martani ga mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma, Sanata Bello Hayatu Gwarzo kan furucin da ya yi a kwanan baya bisa nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben gwamnan jihar Osun.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, abin bakin ciki ne ganin yadda jam’iyyar PDP a jihar Kano ta shiga cikin rikici yayin da wadanda ke da alhakin gyara jam’iyyar suka shagaltu bisa ganin nasarar wata Jiha tare da barin jam’iyyar cikin wahala a jihar su.

“Abin takaici ne yadda aka bar jam’iyyar PDP ta Kano cikin rudani da wadanda ake zaton za su gyara ta. Haka nan kuma abin takaici ne a lura da cewa, maimakon mayar da hankali wajen dinke barakar da ke akwai a jam’iyyar a jihar Kano, Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya shagaltu da fafutukar ganin wasu sun kai gaci.

A bayyane yake cewa Gwarzo ya kamata da farko ya gyara gidansa kafin ya fara murna domin nasarar da wasu suka samu,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here