Bidiyon Seun Kuti, dan gidan fitaccen mawakin Afrika, Fela Kuti, yana cika baki da cewa ya mari ‘yan sanda masu yawa.
Ko da yake ba a san lokacin da ake nadar faifan bidiyon ba, an ga Seun yana cewa ya mari ‘yan sanda da dama saboda sanin wanene shi.
“Wasu daga cikin ‘yan sanda sun yi ta marin jama’a, sai ku zo Instagram don yin bayani. Ka san ‘yan sanda naw na fallawa mari?” Ya tambaya cikin yaren pidgin.
“Sun ce saboda ni Dan gidan Fela kuti ne. Ba ku sani ba domin Yesu ya mutu dominku? Dole ne ku san ko wanene ku kafin ku yi wani abu. Don haka, na yi hakan ne saboda na san ni ko wane ne. ”…
Idan dai za a iya tunawa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ne ya bayar da umarnin a kamo Kuti bayan an kama shi yana cin zarafin wani dan sanda da ke bakin aiki.
Da yake mayar da martani m a daren Asabar, mawakin ya ce jami’in ya yi yunkurin kashe shi da duk danginsa.
Ya kuma yi ikirarin cewa dan sandan ya ba shi hakuri kuma ya yafe masa.
Kuti ya ce: “Ya yi ƙoƙari ya kashe ni da iyalina. Ina da hujja amma ba ni da kwakkwaran fata. Ya ba da hakuri kuma na amince ba zan kai shi kara ba.
Dangane da umarnin kama shi, mawakin ya ce ya yi maraba da binciken.
“Ina maraba da binciken kuma zan ba da cikakken hadin kai! Ina kuma yi wa sufeton ‘yan sanda da ya gurfanar da duk wanda aka kama da laifi,” ya rubuta.











































