Ma’aikatan Jihar Zamfara Sun Gudanar da Addu’o’i Kan Rashin Biyan Albashin Watanni Uku.

Daruruwan ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara ne suka mamaye filin Sallar Idi da ke Gusau babban birnin jihar don gudanar da addu’o’in ‘AlQunut’ ga al’ummar Musulmin da ke fuskantar mawuyacin hali.

An lura cewa da misalin karfe 10:00 na safiyar karshen mako ne ma’aikatan suka mamaye filin Idi suna neman Allah ya shiga lamarin su domin gwamnatin jihar ta biya su albashi.

Daya daga cikin ma’aikatan, (an sakaya sunansa) wanda ya yi magana a madadinsu, ya bayyana cewa ba a biya ma’aikatan albashin su ba na kusan watanni uku, (Fabrairu, Maris da Afrilu).

Ya bayyana cewa suna neman taimakon Allah kan lamarin da ya shafi ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a jihar.

“Da yawa daga cikinmu sun koma mabarata, ba mu iya cin abinci sau uku a rana da biyan kudin makarantar yaranmu, in ji shi.

“Mun sha wahala sosai saboda wasu akan wannan gwagwarmaya, da yawa sun rasa rayukansu.

Ya kuma kara da cewa, “Mun taru ne ba tare da la’akari da addini ba domin mu nemi taimakon Allah ga kowa da kowa,” in ji shi.

Shima wani ma’aikacin gwamnati, yace gwamnan yana huce haushinsa kan rashin nasarar sa a babban zaben kasar.

Da Jaridar Solacebase ta tuntubi mai baiwa Gwamnan Zamfara shawara na musamman kan wayar da kan jama’a da kafafen yada labarai, ya ce al’ummar jihar su yi godiya ga gwamnan domin bai taba kasa biyan albashi ba a shekaru hudu da suka wuce.

Baffa ya ce jihar na fama da matsalar kudi kamar sauran jihohin tun watan Disambar bara.

Da aka tambaye shi ko me ya sa batun rashin biyan albashin ma’aikatan gwamnati ke tafe bayan kammala zabe, sai ya musanta rade-radin da ake yi na cewa ba a biyan ma’aikata albashin ne saboda Gwamna ya fadi zabe, yana mai alakanta irin wadannan kalamai ga masu cin zarafi.

“Amma ba gaskiya ba ne duk ma’aikatan gwamnati da ba a biya su albashin watanni uku ba, mun fara biya, har ma wasu ma’aikatan sun samu albashin su jiya Asabar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here