Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 54.99.
An gudanar da bikin rattaba hannun a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa da ke Abuja, tare da halartar shugabannin majalisar dokokin kasar nan da sauran manyan jami’an gwamnati.
A ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu ne majalisun biyu suka amince da kasafin, bayan da ‘yan majalisar suka amince da kara masa kudi daga kasafin farkon naira tiriliyan ₦49.7 da shugaban kasa ya gabatar.
Labari mai alaƙa: Majalisar wakilai ta amince da Naira Tiriliyan 54.99 a matsayin kasafin kudin 2025
Dokar Kasafin Kudi ta 2025 tana wakiltar karin kashi 99.96% daga kasafin kudin 2024 na ₦27.5 tiriliyan.