Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben gwamna a 2019 ba, da cewar an ƙaƙabawa jama’a shi ne da karfi da yaji.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta bayyana cewa, sabanin ikirari da ya yi a wata hira da ya yi da wata jarida ta kasa, Kwankwaso ya gudanar da wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, galibi ba su da ko da masu kada kuri’a.
Ya ce a fili yake cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a aka ce akasarin akwatunan zabe an cika su, sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba ko kuma ba a kama masu kada kuri’a ba.
Yace a don haka dole ne ta soke sakamakon daga cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda a matsayinsa na shugaba da ke da hannu a cikin harkokin zabe, Kwankwaso har yanzu yana fafatawa da sakamakon zaben da hukumar zabe ta gudanar da kotuna ta tabbatar.
Kwamishinan ya ce kwanaki kadan da suka gabata, Kwankwaso ya shiga kafafen yada labarai yana gargadin mabiyansa kan kalaman da ba su dace ba amma sai shi kuma ya rika zage-zagen da ba su dace ba.
”Abun takaici ne yadda a matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi” in ji Sanarwar.
Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.
A cewar ta a fili take cewa Kwankwaso ya fahimci gwamnatin Ganduje ta tsere wa sa’a wajen shimfiɗa muhimman ayyuka ga jama’a, shi ya sa yake ganin ana ƙoƙarin shafe abun da yake ganin ya yi a nasa
”Kwanan nan aka ji shi yaa jan hankalin magoya bayansa su kaucewa furta miyagun kalamai amma sai ga shi ya ɓige da yi shi da kansa, ko kaɗan wannan bai dace da shi ba”.













































