‘Yan uwa guda uku sun rasa rayukansu bayan jirgin ruwa ya kife a Dam din Tiga dake Karamar Hukumar Tudunwada ta Jihar Kano.
SolaceBase ta rawaito ce an gano wadanda suka mutu da sunaye Murjanatu, Atikatu da Bilkisu, wanda aka fi sani da Amira, dukkansu daga garin Yalwan Rugu-Rugu.
An ruwaito cewa lamarin ya faru da kusan misalin karfe 2:00 na rana ranar Asabar, lokacin da jirgin ruwa da ke dauke da ‘yan matan uku ya kife a cikin dam din.
Shugabar Karamar Hukumar Tudunwada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin sakon ta’aziyya da ta wallafa a shafukan ta na sada zumunta.
Sa’adatu ta mika sakon ta’aziyya ga mutanen Yalwan Rugu-Rugu, musamman iyalan mamatan.
Ta yi addu’ar Allah Ya karbi su a matsayin shahidai, ya kuma gafarta musu kurakuransu yasa sun huta.
Ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyayensu, ‘yan uwa da abokan su karfi da hakuri kan wannan rashi, tare da rokon Allah ya kiyaye sake faruwar irin wannan mummunan abu a nan gaba.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan yadda hadarin ya faru ba.












































