Gwamnatin Tarayya ta rufe kwalejojin gwamnati guda arba’in da ɗaya a faɗin ƙasar saboda matsalar tsaro da ta sake kamari bayan sace ɗalibai a Maga, Jihar Kebbi da na Jihar Neja.
Wannan umarni ya fito ne ta cikin wata takarda da Ma’aikatar Ilimi ta tura wa dukkan shugabannin makarantun gwamnatin tarayya, wadda Daraktar Ilimi ta makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir ta sanya hannu, inda ta umurci makarantun da ke jerin su rufe nan take domin kauce wa sake faruwar matsalar tsaro.
Takardar ta bayyana cewa Ministan Ilimi ya amince da rufe makarantun da abin ya shafa domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin ɗalibai da malamai, tare da bukatar shugabannin makarantun su bi umarnin yadda ya dace.
Haka kuma takarda ta bayyana cewa wannan mataki na rufe makarantun zai taimaka wajen dakile barazanar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar, tare da tabbatar da cewa ba a sake samun wata matsala ba a cikin makarantun gwamnatin tarayya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa makarantun da abin ya shafa sun haɗa da Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Minjibir, Kwalejin Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya Ganduje, Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Zariya, da Kwalejin Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya Kafanchan, tare da sauran makarantun da ke Jihar Katsina, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Yobe, Adamawa, Bauchi da Gombe.
Sauran makarantun sun haɗa da Kwalejin Gwamnatin Tarayya Ilorin, Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Omu-Aran, Kwalejin Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya Gwanara, Kwalejin Gwamnatin Tarayya Ugwolawo, Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Bwari, Kwalejin Gwamnatin Tarayya Rubochi, Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Potiskum, Kwalejin Gwamnatin Tarayya Buni Yadi, Kwalejin Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya Gashua, da sauran makarantun da aka bayyana a jerin.













































