Ƴan bindiga da suka sace kimanin masu ibada 35 daga cocin Christ Apostolic Church da ke garin Eruku a karamar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara sun nemi a biya su Naira miliyan 100 kan kowane mutum guda.
A ranar Talata da yamma ne ’yan bindigar suka kai hari cocin, inda suka hallaka wasu daga cikin masu ibadar sannan suka yi awon gaba da wasu.
Bidiyon da aka dauka a yayin harin ta hanyar watsa shirye-shiryen kai tsaye ya nuna yadda masu ibadar ke gudanar da hidimar su kafin daga baya a ji harbe-harbe a wajen cocin.
Rahotanni daga jaridar Punch sun nuna cewa iyalai da shugabannin al’umma da dama sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwa sun fara tuntubar iyalan wadanda aka sace ta wayar wadanda abin ya rutsa da su.
Sakataren cocin, Josiah Agbabiaka, ya ce an fara samun kiran neman fansa daga masu garkuwa da mutane ga wasu iyalai.
Punch ta rawaito cewa an nemi iyalan rukuni na farko na mutane 11 su biya Naira miliyan 100 kowanne mutum.
Haka kuma, Olusegun Olukotun, Olori Eta na garin Eruku, wanda iyalansa hudu na daga cikin wadanda aka sace, ya bayyana cewa masu garkuwa suna kiran neman fansa ne ta tsarin rarraba rukuni-rukuni.
Olukotun, wanda yake cikin cocin da iyalansa a lokacin harin, ya tsere ta taga, yayin da aka yi awon gaba da sauran iyalan nasa.
A gefe guda, Sarkin Eruku, Oba Busari Olarewaju, ya roki gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha da su dauki matakin gaggawa don kubutar da mutanen.
Sarkin ya yabawa matakin gaggawar da sojoji suka dauka ta hanyar shiga garin bayan ziyarar Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Laraba, amma ya ce ana bukatar ƙarin kokari.
Ya ce zuwan sojoji daren Laraba ya ba su kwarin gwiwa cewa gwamnati na daukar mataki, amma ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara matsa kaimi domin ganin an ceto mutanen cikin gaggawa.













































