Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), ta musanta shirin gudanar da babban taronta na kasa a ranar 19 ga watan Fabrairu, inda ta bayyana shi a matsayin labaran karya.
Mista Kabiru Gwangwazo, Sakataren Yada Labarai na kasa, PRP ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa.
Gwangwazo ya ce wata kungiya da ke ikirarin yin aiki a madadin shugabannin jam’iyyar ne suka sanar da jam’iyyar wani jita-jita.
“Ta wannan sanarwar muna sanar da daukacin ‘ya’yan jam’iyyar PRP da sauran jama’a cewa taron na kasa na bogi ne wanda aka shirya da nufin yaudarar mutane hankali.
“An sanar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da dukkan hukumomin da abin ya shafa, da ‘yan sanda da sauran su a hukumance, kuma tabbas za su yi hukunci mai tsanani kan masu hannu a cikin shirya wannan haramtaccen taro.
Gwangwazo ya ce jam’iyyar PRP a ko da yaushe ita ce fata ga marasa galihu a Najeriya tun bayan da aka dawo da rijistarta da kuma taron wakilai na kasa (NDC) da aka gudanar a watan Satumbar 2018.
Ya ce an zabi shugaba, Malam Falalu Bello a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa kuma shugaban BOT Marigayi Alhaji Balarabe Musa wadanda suka yi ta kokarin ganin sun samar da ingantaccen tsari a fadin jihohin kasar nan.
Ya kuma ce jam’iyyar ta samu halaccin cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, kuma ya zuwa yanzu jam’iyyar PRP a karkashin Bello ta gudanar da tarukan taro inda a yanzu duk shugabannin zartarwa na jihohi suke.
Gwangwazo ya ce ana ci gaba da tuntubar juna tare da kungiyoyi da dama da ke da sha’awar hada kai da jam’iyyar PRP domin ceto Najeriya da ‘yan Najeriya tare da kai su ga kasar alkawari.










































