Mutane 17 sun kone kurmus a wani hatsari a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

1EC8B43B B788 4001 9884 799BDCDB50F9
1EC8B43B B788 4001 9884 799BDCDB50F9

Akalla mutane 17 ne suka kone kurmus a ranar Juma’a a wani hatsari da ya rutsa da wata motar bas kirar Mazda da wata tanka a gadar Isara dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a Ogun, Mista Ahmed Umar, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) faruwar lamarin a Abeokuta.

Umar ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5.00 na safe, inda ya ce ba a iya tantance adadin mutanen da hatsarin ya rutsa da su.

Ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da motar bas din ke kokarin shiga Ibadan, tayin da tankar ke kokarin fita, wanda ya yi sanadin taho mu gama inda nan take  gobara Ta tashi.

Ya bayyana motocin biyu da hatsarin ya rutsa da su, wata motar bas kirar Mazda ce mai lamba ZT 28 KLD da wata tanka mara lamba.

Jami’in FRSC ya bayyana cewa balagagge namiji daya ne, babba mace daya da kuma yaro mace daya kadai aka iya tantance a cikin wadanda abin ya shafa.

Umar ya ce an sanar da ofishin ‘yan sanda na shiyya ta Isara faruwar lamari.

Kwamandan sashin ya ce idan har an bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa za a iya kaucewa afkuwar hatsarin.

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu, ya kuma umurce su da su tuntubi hukumar FRSC Ogere, domin karin bayani game da hadarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here