Najeriya da wasu kasashen Afirka biyar za su fara samar da allurar rigakafin COVID-19 – WHO

FB6D0468 0F02 4033 A8CA E1F00DE59B1D
FB6D0468 0F02 4033 A8CA E1F00DE59B1D

An zabi Najeriya da wasu kasashen Afirka biyar don fara samar da allurar rigakafin COVID-19, inda nahiyar ke da karancin samun allurar.

“A yau ina farin cikin sanar da kasashe shida na Afirka  za su karbi fasaha daga cibiyar don samar da nasu rigakafin mRNA, kasashen sune: Masar, Kenya Najeriya, Senegal Afirka ta Kudu, da Tunisia,” Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Ghebreyesus, ya sanar a ranar Juma’a.

A cewar hukumar ta WHO, an zabo su ne a matsayin wadanda suka fara samun fasaha daga cibiyar rigakafin mRNA ta duniya, a wani yunkuri na tabbatar da cewa nahiyar Afirka za ta iya yin nata allurar don yakar COVID da sauran cututtuka.

“Muna sa ran za a fara gwajin asibiti a kashi na 4 na wannan shekara, tare da amincewa da ake sa ran a shekarar 2024.

Muna sa ran fa’idar wannan shiri zai wuce # COVID19, ta hanyar samar da wani dandali na alluran rigakafin wasu cututtuka da suka hada da zazzabin cizon sauro da tarin fuka”.

“WHO za ta yi aiki da kamfanoni da gwamnati a kowace kasa don samar da taswirar horo da samarwa, bisa la’akari da bukatunsu da karfinsu.

A ranar alhamis, Najeriya ta sami sabbin mutane 45 da suka kamu da cutar, wanda ya kawo adadin wadanda aka tabbatar a kasar zuwa 254,182.

230,530 an ce sun warke, yayin da aka samu rahoton mutuwar mutane 3,141 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.

An samu sabbin masu dauke da cutar su  45 daga jihohi takwas – Legas (18), Cross River (7), FCT (7), Oyo (5), Kano (3), Nasarawa (3), Ekiti (1) da Rivers (1).

Ana ci gaba da samun karancin rigakafin A duk faɗin duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here