Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi goron gayyatar da shugaban kasar Czech, Milos Zeman ya yi masa na ya ziyarci kasarsa a shekarar 2022.
Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a mai taken, ‘Shugaba Buhari da sauran mambobin kungiyar G4 sun bullo da sabbin dabarun magance rikice-rikice a Afirka,’’ ta bayyana hakan.
Wannan na zuwa ne lokacin da Buhari ya yi marhabin da sha’awar shugaban na Czech don ƙarin haɗin gwiwa tsakanin kasashen biyu domin samar da kayan aiki da kuma inganta tsaro a Najeriya.
Sanarwar ta ce, ”Buhari da takwaransa na kasar Czech, wadanda suka gudanar da wata tattaunawa a ranar Alhamis a birnin Brussels na kasar Belgium, sun sabunta alkawarin da suka yi kan tsarin hadin gwiwa don inganta dangantakar da ke tsakaninsu ta fuskar diflomasiyya da kuma ci gabab jama’a.
‘’Ya kuma bayyana irin shiri da ya yi na samar da hadin gwiwa da Najeriya a fannin Noma da Lafiya sannan kuma ya yanke shawarar shirya taron tuntubar shugabannin kungiyar ta EU don taimakawa wajen tsara ajandar shugabancinta tun farko.













































