Buhari ya aikawa majalisa sunayen kwamishoni a hukumar zabe da hukumar kidaya

9384361C 6C0F 49F8 83C0 405832F44EE0
9384361C 6C0F 49F8 83C0 405832F44EE0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turawa majalisar Dattawa sunayen mutane 6 wanda yake neman a sahale masa ya nada su a matsayin manyan kwamishoni, da kuma mutum daya a matsayin karamin kwamisha a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Mutanen da shugaba Buhari ya tura da sunayen su sune: Malam Mohammed Haruna daga jihar Niger, sai May Agbamuche Mbu daga jihar Delta, da kuma Okeagu Kenneth Nnamdi daga jihar Abia, sai A.B. Alkali daga jihar Adamawa, sai Farfesa Rada Gumus daga jihar Bayelsa, da kuma Sam Olumeku daga jihar Ondo State.

Haka kuma Buhari ya nemi majalisar ta amince masa ya nada kwamishoni a hukumar kidaya ta kasa.

Kwamishinonin sune: Benedict Opong daga Akwa Ibom, Gloria Izofor Mni daga Bayelsa, Patricia O. Iyayan Kuchi daga Benue, Bala Haliru daga Kebbi State da kuma  Iyatayo Oyetunbi daga jihar Oyo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here