An garzaya da Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, Abdulrasheed Bawa, zuwa asibiti bayan da yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Bawa yana jawabi ne a wajen wani taro na bikin Ranar Shaidar dan Ƙasa a lokacin da kwatsam ya daina Magana, inda ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana cewa, “Don Allah, a yi hakuri, ba zan iya ci gaba ba.”
Yana magana ne game da wani mutum da hukumar ta kama a Ibadan, jihar Oyo, da layin waya na SIM guda 116 lokacin da lamarin ya faru.
Karanta Wannan: 2023: Za Mu Baiwa Jonathan Damar Tsayawa Takara Idan Ya Dawo Jam’iyar Mu- APC
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, da wasu manyan jami’ai ne suka taimaka masa a wurin zama.
Saidai daga bisano Jagoran Taron wato (MC) ya ba da sanarwar cewa yanayin Bawa ya dawo daidai.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Shugaban EFCC a yanzu ya warware,” in ji shi.
Amma wadanda suka hanzarta fitar da shi daga wajen taron har zuwa lokacin hada wannan labari ba su koma zauren ba, kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta ruwaito.
Akwai Karin bayani nan gaba……













































