Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma APC.
Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya karbe shi.
Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC, kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatar da shi ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Mista Fani Kayode ya ce hukuncin ubangiji ne ya rinjaye shi wajen yanke shawarar shiga APC ne don taimakawa hadin kan kasar nan, ya kara da cewa yana adawa da duk wani abin da zai haifar da wargajewar Najeriya.
Karanta Wannan: YANZU-YANZU:Shugaban Hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa, Ya Yanke Jiki Ya Faɗi
Ya bayyana cewa ficewar wasu gwamnoni uku daga PDP zuwa APC ne ya taka rawa matuka wajen jan ra’ayin shi.
Gwamnonin da ya ambata sune Dave Umahi na jihar Ebonyi, Ben Ayade na jihar Cross River da Bello Matawale na jihar Zamfara.
Ya ci gaba da cewa yana da abokai a cikin jam’iyyar kuma yana neman gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da su shiga jam’iyyar mai mulki.













































