A cikin wata sanarwa da Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta bayar, mai ɗauke da sa-hannun shugaban shiyyar Arewa-maso-yamma na hukumar, Alhaji Umar G. Fage, hukumar ta ce fassara finafinan ya saɓa wa dokar ta ne.
Takardar sanarwar da hukumar ta turo wa mujallar Fim, mai taken “Fassarar Finafinan Indiya Da Hausa”, ta na ɗauke da kwanan wata 15 ga Nuwamba, 2022.
A ciki ta faɗa wa masu harkar finafinai cewa: “Doka ta 85 ta 1993 wato ‘CAP N40 LFN 2004 da Ƙa’idojin 2008’, a ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Al’adu ta Tarayyar Nijeriya, ita ce ta kafa Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa.
“Hukumar ta na da hurumin tsaftace ayyukan fim da bidiyo (wato masana’antar nishaɗantarwa).
“Aikin hukumar ne kamar haka:
“Ta ba da lasisi ga mutum ya bayyana ayyukan sa na fim da bidiyo; ta ba da lasisi ga gida domin nuna ayyukan fim da bidiyo; ta tace ayyukan fim da bidiyo; ta tsaftace tare da kafa ƙa’idojin kula da lafiya a wuraren haska su; ta tsaftace tare da sanya ido kan abubuwan da ake haskawa a gidajen sinima; kuma ta gudanar da duk wasu ayyuka makamantan waɗannan da aka ga sun zama tilas ko sun dace wajen cikakkiyar gudanuwar dukkan ko wani haƙƙi da wannan dokar ta ɗora mata.
“A bayyane ya ke ƙarara cewa dokar ta bayyana abubuwa kamar haka:
“Ba a yarda wani mutum ya shiga harkar rabawa ko nuna wani aikin fim ko na bidiyo ba har sai ya samu lasisin yin hakan daga hukumar.
“Ba a yarda wani mutum ya nuna ko ya sa a nuna wani fim ba tare da ya samo satifiket ɗin tacewa daga hukumar domin ya nuna shi ba.
“To amma ofishin shiyyar Arewa-maso-yamma na hukumar ya lura tare da damuwa ƙwarai kan yadda wasu mutane su ka shiga harkar kwafa, fassarawa, da rarraba finafinan ƙasashe waje zuwa harshen mu na gado, wanda yin hakan ya saɓa wa sashe na 25(1), 33(1), 56 da 1(3) 5(1) na dokar da ta kafa hukumar, wato Dokar 1993 CAP N40 LFN 2004 da Ƙa’idojin 2008.
“A bisa wannan sanarwa, hukumar ta gargaɗi irin waɗannan mutanen da su kiyayi aikata abin da su ke yi wanda ke iya jawo matsala ga masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya.
“Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa ba za ta iya ci gaba da amincewa da wannan abu ba daga kowane mashiryin fim maras gaskiya.
“Fassarar finafinan Indiya zuwa Hausa ya saɓa wa doka, kuma duk wanda aka kama ya na aikata hakan zai fuskanci shari’a.
“Don haka wannan gargaɗi ne gare ku. Mun gode.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa hukumar ta aika da sanarwar ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar fim irin su furodusoshi, daraktoci, masu sayar da fim, masu nuna fim, da ƙungiyoyin ‘yan fim.













































