Yan Sanda Sun Tabbatar da Yin Harbe-Harbe a Wata Jam’iyyar Najeriya

police 1 750x430 1
police 1 750x430 1

Hukumar ‘yan sanda, ranar Talata a Kalaba, ta tabbatar da faruwar harbe-harben bindiga a harabar jami’ar jihar Kuros Riba. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, wanda ta tabbatar da aukuwar lamarin tace an yi harbe-harbe a jami’ar ne ranar Litinin.

Mis Ugbo, Sufuritandan ‘yan sanda tace wani ɗalibin ajin ƙarshe a makarantar ya samu raunin harbi lokacin da lamarin ya faru, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ta alaƙanta faruwar harbe-harben da ayyukan ‘yan daba da asiri, inda ta kara da cewa ‘yan sanda zasu zakulo duk masu hannu a hukunta su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here