Aisha Buhari: Kotu ta aike da Aminu Muhammad gidan yari

4e5ef8fa0a8bb394
4e5ef8fa0a8bb394

An gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, a gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

”Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.”

”Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,” in ji CK Agu.

Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace ” yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.”

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here