Majalisar Wakilai ta Kasa ta gayyaci Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da shugabannin tsaro da su bayyana gaban majalisa kan karuwar lamarin rashin tsaro a fadin kasar.
Majalisar ta zartar da kudurin ne a zaman da ta yi a ranar Talata bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum daga Zamfara, Sulaiman Gumi ya gabatar.
Shugabannin tsaro da aka gayyata sun hada da Babban Hafsin Tsaro, Olufemi Oluyede da Waidi Shaibu Hafsin Sojin Kasa da Idi Abbas Hafsin Sojan Ruwa da kuma Sunday Aneke Hafsin Sojan Sama.
‘Yan majalisar sun kuma gayyaci Adeola Ajayi, Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Taiwo Oyedele Ministan kudi da kuma Christopher Musa, Ministan Tsaro.
Ana sa ran Oyedele zai bayyana a gaban ‘yan majalisa kan kudaden da aka fitar don siyan kayan aikin soja da ake bukata wajen magance kalubalen tsaron kasar.
Majalisar ta umarci shugabannin tsaro su bayyana a gabanta a ranar Laraba, zaman da za a yi cikin sirri













































