Najeriya ta tura sojoji 157 don samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Sojojin, Sudan Ta Kudu, Najeriya, zaman lafiya, tura
Rundunar sojin Najeriya ta gargadi sojoji 157 da ta tura zuwa aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu da su kasance jakadu nagari na kasarsu...

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi sojoji 157 da ta tura zuwa aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu da su kasance jakadu nagari na kasarsu.

Sojojin sun kammala atisayen turawa sun kuma shirya aikin wanzar da zaman lafiya a Abyei da ke Sudan ta Kudu.

Hukumomin sojojin sun shawarce su da su guji yin lalata da kuma safarar miyagun kwayoyi, inda suka ce irin wannan abu na iya bata sunan Najeriya.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya hana ministoci da jami’an gwamnati zuwa kasashen waje

Babban Hafsan Sojoji, Manjo Janar Boniface Sinjen, ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a wajen bikin yaye daliban daga horon da suka yi tun kafin a tura su a cibiyar shugabanci da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai (MLAILPKC) da ke Jaji a jihar Kaduna.

Dakarun sun kunshi jami’ai 15 da sojoji 142, Janar Sinjen ya tunatar da sojojin da su kasance akoda yaushe masu bin ka’idojin aiki tare da kiyaye ‘yancin ɗan adam da kuma mutunta bambancin yanayin aiki.

Karin labari: Rikici ya barke tsakanin kungiyar NLC da jam’iyyar LP

Shugaban rundunar ya ce taron yaye rundunar ya nuna himma da kwazon rundunar sojin Najeriya na tura dakaru masu inganci a matsayin wani bangare na gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ya yi nuni da cewa, manufar tsaron kasa ta Najeriya ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Afirka tare da ba da muhimmanci ga yankin yammacin Afirka.

Sinjen ya ce wannan ne dalilin da ya sa Najeriya za ta ci gaba da neman zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyar ba da gudummawa da kuma shiga ayyukan tallafawa zaman lafiya a duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here