An bude shagon shan barasa a kasar Saudiyya, irinsa na farko a tsawon shekarau 70.
An dai takaice shagunan ne ga jami’an huldar jakadancin kasashe da ke Saudiyyar.
Ana dai yi wa wannan mataki kallon wani kokari a kasar da ta haramta sayar da shan barasa tun shekarar 1952.
Karin labari: Najeriya ta tura sojoji 157 don samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
Tun dai a watan Janairu ne kasar ta sanar da cewa za ta bude shagunan sayar da barasa ga wasu kayyadaddun mutanen da ba Musulmi ba a birnin Riyadh.
Yanzu dai jama’a na dasa ayar tambaya ga yunkurin kasar ta Saudiyya, inda suke neman sanin ko dai akwai yiwuwar kara fadada damar shan barasa a kasar fiye da takaice shi ga jami’an huldar jakadanci.