Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Dakta Zaid Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar (KIRS).
Gwamnan ya kuma amince da nadin Kassim Ibrahim a matsayin babban darakta na hukumar tara kudaden shiga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata.
Karin labari: CITAD Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Kara Harajin Sadarwar a Najeria
Sanarwar ta ce sabon tsarin gudanarwa ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar tsohon shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar Kano Alhaji Sani Abdulkadir Dambo ya koma aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari.
Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin ke yi na inganta kudaden shigar da jihar ke samu a cikin gida.