Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa 30 ga watan Satumba, 2024.
Babban bankin ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 6, ga watan Mayu 2024, wanda Adetona Adedeji, daraktan kula da harkokin banki na CBN ya sa hannu.
A ranar 1 ga watan Mayu, bankuna sun dawo da tattara kudaden sarrafawa a kan ajiyar kuɗi.
Karin labari: Dalilin da yasa Gwamnan Kano ya cire shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar
A bisa umarnin, kashi 2 cikin 100 za a caje su a kan adibas sama da Naira 500,000 ga daidaikun mutane, yayin da masu asusun ajiyar kamfanoni za a caje kashi 3 bisa 100 na ajiya sama da N3,000,000.
A bisa sabon takardar da aka bai wa cibiyoyin hada-hadar kudi da kuma cibiyoyin da ba na kudi ba, CBN ya ce an dakatar da kudaden sarrafa su.
Babban bankin na CBN ya umarci cibiyoyin hada-hadar kudi da su ci gaba da karbar duk wasu kudade daga jama’a ba tare da wani caji ba har zuwa karshen kwata na uku.