Duk da tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da shi a Najeriya. Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa wani mai sana’ar POS mai suna Mohammed Abdulrahman, ya mayar da Naira miliyan 10 bisa kuskuren da akayi na turawa cikin asusunsa.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Ya ce mai kudin dan kasuwa ne a kasuwar Dawanau da ke cikin birnin Kano.
Karin labari: An ƙayyade wuraren sayar da burodi da man fetur a Zamfara
Kiyawa ya ce, mai POS din ya shaida musu yadda mai kudin ya yi niyyar tura kudi Naira 10,000 amma ya yi kuskure ya tura Naira miliyan 10 zuwa asusun sa.
“Kamar yadda mai POS ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa akwai wani kwastomansa da ba’a san inda yake ba, ya tura masa kudi bisa kuskure har naira miliyan goma 10,000,000 a maimakon naira dubu goma N10,000″ in ji sanarwar.
“Kuma sai da ‘yan sanda suka gudanar da bincike na tsawon watanni 3 wajen gano wanda ya riski kudaden. Bayan samun dukkan hujjoji, CP Gumel ya yiwa mai sana’ar POS da tawagar ‘yan sanda da na CID godiya domin nuna gaskiya da rikon amana da kwarewa tare da karfafawa sauran mutane gwiwa da su bi wannan hanya mai inganci.
Karin labari: Akwai shirin tura jami’an tsaron Kenya zuwa Haiti – Ruto
Tun a ranar 21 ga watan Disambar 2023 ne wani jami’in hulda da jama’a na POS wanda aka fi sani da Mohammed Sani Abdulrahman, mai shekaru 37 da ke Kurna Asabe a jihar Kano, ya kai karar kansa a hedikwatar ‘yan sanda ta Bompai” Kiyawa ya bayyana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “wani daga cikin kwastomominsa ya biya kudi fiye da kima a kasuwancin sa na POS har naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in 9,990,000 yayin da yake son yin musayar kudi ta yanar gizo zuwa naira dubu goma 10,000 kawai, wanda daga nan aka yi kuskuren tura adadin kudi na naira miliyan goma 10,000,000.
Karin labari: Za’a kai Falasɗinawa cibiyoyin jin-ƙai kafin ƙaddamar da hari a Rafah
Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya umurci tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin SP Abdulwahab Zubairu daga sashin CID da su gudanar da bincike na gaskiya tare da jami’an tsaro, don gane mai shi da mayar da kudin” a cewar sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta kara bayyana cewa “a ranar 14 ga watan Maris 2024 ne aka kammala binciken ta hanyar gano ainihin mai kudin, wanda dan kasuwa ne a kasuwar Dawanau ‘yan hatsi.
Karin labari: “Ba za mu biya ƴan bindiga ko sisin kwabo ba” – Tinubu
Bayan an gudanar da bincike mai zurfi tare da gamsuwa da hujjojin mallakarsu, an mayar da kudaden, fiye da miliyan tara, naira dubu dari tara da casa’in 9,990,000 zuwa asusun mai shi.”
Sai dai an bayyana cewa an baiwa mai sana’ar POS din la’adar tsuntuwa kyautar kudi naira dubu dari 500,000 kyauta.
Sanarwar ta kara da cewa “mai asalin kudin ne ya bada wannan kyauta ga mai POS din ta hanyar yabawa saboda murna da jindadi” in ji sanarwar.
A karshe mai kudin ya kuma godewa CP saboda gaskiyarsa da amincinsa da kuma nuna kyakkyawan misali ga wannan mutum.