Shugaban Kenya William Ruto ya tabbatar da shirin tura jami’an ‘yan sanda zuwa Haiti da zarar an kafa majalisar shugaban kasa ta rikon ƙwarya.
Duk da jinkirin da aka samu tun farko sakamakon murabus din Firaministan Haiti, tattaunawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya mayar da hankali kan gaggauta tura sojojin.
Ruto ya jaddada aniyar Kenya na jagorantar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Haiti domin maido da zaman lafiya da tsaro.
Karin labari: ‘Yan bindiga sun sake kai hari Kajuru tare da sace mata 7
Sai dai kuma kafa majalisar na fuskantar adawa daga wasu jam’iyyun siyasa, lamarin da zai iya tsawaita tsarin
Idan aka kafa majalisar za ta nada firaminista na rikon kwarya tare da haɗa kai da rundunar ‘yan sandan kasashen duniya da Kenya ke jagoranta domin magance tashe-tashen hankulan gungun jama’a.