Kenya za ta zamanantar da makaman yakin sojinta

355161669 591536893151007 8484733943120889201 n
355161669 591536893151007 8484733943120889201 n

Ministan tsaron kasar Kenya Aden Duale ya ce nan da watanni uku masu zuwa gwamnatin ƙasar za ta zamanantar da makaman sojin ƙasar, don dakile hare-hare da kungiyar al-Shabab da ke Somaliya mai makwabtaka ke kaiwa cikin kasar.

A baya-bayan nan wani hari da mayaƙan suka kai gundumar Madera ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku ciki har da ‘yan sanda biyu.

Kimanin jami’an tsaro 22 ne aka kashe cikin makonni biyun da suka gabata sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a yankin Lamu da ke gabar teku da kuma gabashin Garissa da ke kan iyaka da Somaliya.

“Daga cikin makaman har da masu gano abubuwan fashewa da aka dasa a ƙarƙashin ƙasa”.

Ana ci gaba da shirye-shiryen sake bude kan iyakar kasashen biyu a hukumance, karon farko cikin shekaru goma, lokacin da sojojin Kenya suka fara kai farmaki kan kungiyar al-Qaeda da ke Somaliya.

Yaƙin soji kan al-Shabab da sojojin Somaliya suka fara a watan Agustan da ya gabata ya janyo hasarar yankuna masu yawa ga kungiyar ta’addanci.

Ana sa ran sojojin Kenya za su shiga kashi na biyu na wannan farmakin, lamarin da ya sa al-Shabab ta zafafa kai hare-hare a Kenya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here