‘Yan bindiga sun sake kai hari Kajuru tare da sace mata 7

'Yan bindiga, Kujuru, mata, sace, hari
‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya,..

‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya, inda suka kashe mutum daya da kuma yin garkuwa da wasu mutane 8.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewar ‘yan bindigar sun kashe Christopher Zamani da raunata wata mata Mary Isah wacce ke kwance a wani asibiti da ke Marabar Kajuru.

Haka nan ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu matan da suka hada da Tina Bulus da Alice Joshua da Sarah Micah da Jenet Amos da Martha Peter da Rita Geoffrey da Favour Ado sai kuma namiji daya Kaduna Fidelis.

Karin labari: Za’a kai Falasɗinawa cibiyoyin jin-ƙai kafin ƙaddamar da hari a Rafah

A wani labarin kuwa, mutane 24 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a garin Buda a ranar Litinin din da ta gabata duk a karamar hukumar ta Kajuru, sun kubuto daga hannun wadanda suka yi garkuwa dasu.

Wani mazaunin garin Benjamin Yuhana, ya ce mutanen sun dawo gida ne ba tare da an biya ko sisin kobo ba a matsayin kudin fansa, duk da cewa har yanzu akwai wasu da dama a hannun masu garkuwa da mutanen.

Karin labari: Da Dumi-dumi: Najeriya ta bude kan iyakokinta da Nijar

A baya-bayan nan dai, jihar Kaduna ta na fuskantar kalubalen tsaro da garkuwa da mutane, daga cikin akwai na sace dalibai 287 da ‘yan bindiga suka yi a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun.

A lokacin wata zantawa da aka yi da kwamishiniyar kula da jindadi da walwalar al’ummar jihar Kaduna Hajiya Rabi Salisu, ta ce gwamnatin jihar na aiki tukuru don ganin an kubutar da daliban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here